Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Isma’il Na-Abba Afakallahu, zai Angwance tare da Tsohuwar Jarumar Finafinan Hausa Rukayya Dawayya.
Za a daura auren ne, a ranar 4 ga watan Nuwamba 2022, da misalin karfe 2pm na rana, a Masallacin Juma’a na Tishama da ke garin Kano.
Kamar yadda Shugaban tace fina finai na kannywood Ismail Na Abba Afakallahu ya bayyana a shafinsa na sada zumuta
“Alhamdulilah muna gyatar yan uwa da Abokan Arziki idan ba’a samu dama ba ayi mana Addu’a”