Hankalin “yan Tiktok ya tashi bayan an kama Mubarak UniquePikin

Ga duk mai bibiyar dandalin yasan Mubarak da kuma irin Shirin sa da yake yi tare da Kaninsa wanda yake kira da Na’ibi.


Bayan Mubarak din yana tsare a wajen hukuma dubban “yan uwa da Abokan Arziki ne suka dinga taya jaje tare da mika kokon bara zuwa Gwamnan na jihar ta Kano domin yayi masa afuwa sannan a sako musu dan uwa.


Cikin wadanda suka mika kokon barar sun hada da manyan Abokan sa a sahar irin su Baddo (Ali Nuraddeen),Murja Ibrahim Kunya,MJ Talent,Abba C Sale da dai sauran su.


Ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa.