An kashe wani mutum mai suna Johane Mareya bayan an kama shi yana lalata da wata matar aure a gidan ta, sakamakon haka mijin matar ya kashe shi nan take.
Dan shekara 27 mijin matar mai suna Oscar Mazorodze, dan asalin kauyen Chirindagomo,
a Chief Chireya da ke Gokwe ta Arewa a kasar Zimbabwe, ya fada hannu kuma aka gurfanar da shi a gaban Alkalin Kotun Majistare Mai suna Busani Sibanda, a garin Gokwe bisa zargin kashe Mareya.
An yi zargin cewa ranar 5 ga watan Maris, Mazorodze ya bar wajen aiki da wuri kuma ya dawo gida da misalin karfe 3 na rana,
amma ya tarar da an rufe kofar daki daga ciki, sai ya banke kofar kuma ya wuce zuwa cikin kuryar daki, inda ya yi ido biyu da Mareya yana lalata da matarsa Brenda Dhlodhlo tsirara turmi tabarya.