Kyakkyawar Mata a Abuja Na Neman Wanda Zai Dirka Mata Ciki, Zata Biya N3m - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Kyakkyawar Mata a Abuja Na Neman Wanda Zai Dirka Mata Ciki, Zata Biya N3m

Oct 27, 2022
Abuja – Wata mazauniyar burnin tarayya Abuje dake faɗi tashin zama uwa tana neman kyakkyawan mutumin da zai iya sanya wa ta ɗauki ciki.

Tauraruwar mai amfani da kafar sada zumunta, Uwaoma Susan Joseph, ita ce ta bayyana bukatar matar a dandalin Facebook bukatar matar a dandalin Facebook tare da sakaya bayanan matar legit na ruwaito.


Yayin da matar mai kuɗi ta shirya biyan duƙ wanda ya ci sa’ar gama wannan aikin Naira Miliyan N3m, ta kuma kafa wasu sharuɗɗa yayin gudanar da lamarin.

Susan ta bayyana cewa matar tace duk wanda zai aikin za’a ɗaure masa ido lokacin da zasu sadu. Kuma zata rike shi har sai an tabbatar da ta samu juna biyu.

Babban dalilin da yasa za’a ɗaure wa mutumin ido shi ne don kar nan gaba ya dawo yana nemanta da ɗansa. Susan tace:

        “Suzy dan Allah ki rubutu game da ni, ina bukatar mutumin da zai mun ciki, kyakkyawan mutum. Za’a ɗaure masa fuska duk lokacin da zai kwanta dani kuma zan biya shi.”

“Abinda yasa za’a rufe masa fuska shi ne don kar ya dawo nan gaba yana nemana da ɗan, zan rikenshi har sai an tabbatar na samu ciki sannam zai tafi. Ina zaune a Abuja ni zan kula da komai na kuɗi.”
“Dan Allah ki ɓoye sunana, tace kuɗin da zata biya miliyan uku cas”