Masha Allah wannan abun yayi mana matukar sha’awa farin cikinmu shine Allah ya baiwa duk ya mace miji nagari tayi aure,
a Masana’atar Kannywood kuma sai dauka ake daya bayan daya wannan tabbas duk cikarki ‘ya mace gidan miji yafi miki martaba da kima da daraja a nan duniya da lahira.
“AURE MARTABA
Fitacciyar Jarumar Finafinan Hausa Halima Yusuf Atete, tana dab da zama Amarya nan da kwanaki kalillan.
Za a daura auren Jarumar ne, da Angonta Mohammed Mohammed Kala, a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba 2022, da misalin karfe 10:30am na safe, a Abuja Sheraton Bus Stop, Juma’at Mosque, a garin Maiduguri, da ke Jihar Borno.
Kafin ranar daurin auren za a yi shagulgulan biki, da suka hada da Kwallon Kafa.