Dalilin Da Yasa Na Daina Runguma da sumbuta a fim – Ali Nuhu:Fitattaccen jarumin Fina-finan Hausa da na kudu, Nollywood, Ali Nuhu ya shaida cewa dalilin da yasa ya daina sumbatar mata da runguma a fina-finan Najeriya shine fada da yayi wa kan sa ya daina yin hakan.
Ali ya kara da cewa a matsayin sa na musulmi dan Arewa mai cikakken tarbiyya, shi jakada ne na inda ya fito a ko ina ya ke. Hakan ya sa yayi karatun ta natsu don kiyaywe karantarwar Addinin sa, addinin musulunci da martaba al’umman sa.
“A shekarun baya idan ka lura na yi irin wadannan fina-finai amma daga baya da na ga korafe-korafen mutane, ka ga mutum jakada ne na Arewa…kuma Musulmi…shi ya sa ni yanzu ba na fitowa a irin wadannan fim din.”
Haka Ali Nuhu ya shaida wa BBC Hausa a yar gajeruwar hira da ta yi dashi.
Ali Nuhu ya fito a manyan shirye-shiryen kudu da dama, shirye shiryen da suka yi suna da fice a Duniya. Yana daga cikin fitattun jaruman da suka fara fitowa a fina-finan ‘yan kudu wato Nollywood daga Arewa kuma suka yi fice matuka.
Baya ga zama tauraro, Ali Nuhu ya zama baya goya marayu a farfajiyar Kannywood inda ya kyankyasa jarumai da dama da yanzu suke shanawa a harkar fim ciki akwai Jaruma Rahama Sadau, Nafeesat Abdullahi, Zaharadden Sani, Nuhu Abdullahi da dai Sauransu. Dukkan su dai Kamfanin FKD mallakar Ali Nuhu ne ta yi rainon su har suka girma.
Ali Nuhu yayi fina-finai da ba zai iya fadin yawan su kamar yadda ya fadi sannan kuma ya samu kyaututtuka da lambar yabo masu yawa a gida da wajen Najeriya.