Hukumar Hana Yaduwar Makamai Za Ta Dauki Mutum 300,000 Aiki


Sabuwar hukumar nan mai yaki da yaduwar manya da kananan makamai ta kasa (NATCOM) ta ce ta kammala shirin daukar mutum 300,000 aiki a fadin Najeriya.


Hukumar ta ce za ta dauki mutanen ne sannan ta horar da su don dakile yaduwar makamai a daidai lokacin da ake fama da kalubalen tsaro.


Mai rikon mukamin shugaban hukumar, Otunba Adejare Rewane ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi.jaridar aminiya na ruwaito.


Ya ce hukumar za ta dauki mutum 7,000 aiki a kowacce Jiha ta Najeriya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.


A cewarsa, “Za mu debi mutum 300,000 aiki a fadin Najeriya domin kasarmu ta zauna lafiya.


“Ba kawai daukarsu aiki za mu yi ba, za a ba su isasshen horo. Hakan kuma zai taimaka wajen rage matsalar rashin aikin yi a kasa. Za mu hada kai da sauran jami’an tsaro don ganin mun sami nasara.


“Game da daukar mutum 7,000 da za mu dauka, masu son a dauke su sai su rika duba jaridu domin ganin bayanai da ka’idoji. Amma dai za mu fi ba matasa masu jini a jika fifiko wajen daukar aikin,” in ji shugaban.