Jaruma Aisha Humaira ta hadu da masoyinta da yayo tattaki daga Bauchi zuwa kano

 


Daɗi Da Ƙari Kuma, Ta Ba Wa Mahaifiyar Yaron Jari Domin Su Je Su Cigaba Da Inganta Rayuwarsa.


In ba ku manta ba a ƴan kwanakin nan labarin wani yaro mai suna Adamu ya bazu a kafafen sadarwa na zamani, Yaron da ya taso tun daga Jihar Bauchi ya zo Jihar Kano domin ya ga ƴar Fim ɗin Hausa A’isha Humaira saboda ƙaunar da ya ke mata a cewarsa.



Bayan shafe tsawon makonni biyu Yaron ya na gararamba a kan titi sakamkon ƙwace guzurinsa da ɓatagari su ka yi wanda har hakan ya kai shi ga kwana kan titi ya na gararamba har ya gamu da rashin lafiya ya ke zubar da kumfa daga bakinsa.


Da taimakon Jaridar Dokin Ƙarfe TV da sauran kafafen sadarwa na yanar gizo tuni an samu nasarar ceto rayuwar yaron inda ƴan sanda da sauran Jama’a su ka ɗauke shi su ka kai shi Asibiti, daga nan A’isha Humaira da kanta ta je ta gana da yaron a hannun ƴan sanda inda ta sa aka kawo abinci su ka ci tare da yaron, sannan kuma a daren ta turawa iyayen yaron kuɗin mota su ka taho Jihar Kano domin su tafi da ɗansu gida.


Yanzu haka A’isha Humaira ta ɗauki nauyin karatun Yaron, sannan kuma ta ba wa Mahaifiyar yaron jari domin su samu abin da za su cigaba da inganta rayuwarsa.

Ga cikakken bidiyo anan ku kalla kai tsaye :

Kalli - Bidiyo