Ahmed musa ya gwangwajewa mutane 4 gida a abuja harda mai gadinsa - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Ahmed musa ya gwangwajewa mutane 4 gida a abuja harda mai gadinsa

Dec 30, 2023


Ahmed musa ya gwangwajewa mutane 4 gida a abuja harda mai gadinsa


A ƙoƙarin da ya saba yi wajen tallafawa al’umma, shahararren ɗan ƙwallon ƙafan Najeriya, Kaftin Ahmed Musa MON ya gwangwaje wasu mutane da kyautar gidaje domin su samu muhallin zama da iyalansu, shafin dokin karfe na wallafa a shafinsu na sada zumunta.


Domin Shiga group namu don Jin labarai na Kannywood da sauransu ga link nan


>>> https://chat.whatsapp.com/Fmd72ZV4KczDfumgtH9Qs4


Karanta wannan:


NSIPA zasu Bude portal domin daukar sababbin wadanda zasu ci gajiyar Npower program a watan January 2024 



Daga cikin mutanen da suka samu gidan akwai mai gadinsa wanda ya ba shi gida mai ɗaki ɗaya, da P.A ɗinsa wanda ke zaman abokinsa shi ma ya samu gida mai ɗaki uku, da kuma ma’aikacin ƙungiyar ƙwallon ƙafa shi ma ya samu kyautar gida mai ɗaki uku, sai kuma wata ƴar Jarida wacce suka daɗe tare tun yana ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ita ma ya gwangwaje ta da gida mai ɗaki biyu.


Kaftin Ahmed Musa mutum ne gwarzo wanda ya daɗe yana sanya farin ciki da walwala a cikin zukatan al’umma daban-daban. Ko da a baya-bayan nan ya gwangwaje tsohon ɗan wasan Hausan nan Baba Karkuzo da kyautar gida, ya kuma sanyawa wasu abokansa tun na ƙuruciya gida kyauta ya ba su.


Karanta wannan:


Hukumar Sojan Ruwa sun Bude portal na dauka maaikata NNBTS Batch 36 Ga yadda zaku cika wannan aikin Kai tsaye.


Akwai mutane da dama da suka rabauta da samun gida a sanadiyyarsa, wasu kuma ya tallafa musu ne ta fuskar ilimi, abinci da jarin dogaro da kai da dai sauran muhimman fannoni rayuwa daban-daban. Wanda a sanadiyyar hakan ɗumbin al’umma na cigaba da yi masa godiya da addu’ar fatan alkhairi.