"Ba Buhari Bane" An Gano Wanda Ya Sa Tsohon Gwamnan CBN Ya Canza Takardun Naira a Najeriya
Ana zargin tsohon gwamnan babban banki (CBN), Godwin Emefiele, da canza takardun Naira ba tare za amincewar Muhammadu Buhari ba Jim Obazee, mai binciken CBN mai zaman kansa wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ne ya bayyana haka a rahotonsa A cewar rahoton, Emefiele ya haɗa baki ne da Sabi'u Tunde, hadimi kuma ɗan ɗan-uwan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
ATTENTION
For More Update Join Our WhatsApp Group 👇🏻
https://chat.whatsapp.com/GdEk2acGy4X8FFifk2wRtj
Follow Us On Google News 👇🏻
Join Our Twitter Group 👇🏻
https://t.me/naijastickfansgroup
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Bincike kan yadda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya tafiyar da harkokin CBN na ƙara bayyana musamman kan tsarin canza Naira. Wata gaskiya mai kaɗa hanji daga cikin rahoton binciken ta nuna cewa Emefiele ya canza N200, N500 da N1000 ba tare da amincewar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.
Haka nan kuma ana zargin tsohon gwamnan CBN ɗin da baiwa wani kamfani a Burtaniya aikin buga sabbin kuɗin kan N61.5bn wanda ya saɓa wa umarnin Buhari.
An gano cewa Muhammadu Buhari ya bada umarnin buga sabbin kuɗin a Najeriya amma Emefiele ya yi gaban kansa ya ba kamfanin De La Rue aikin. Wanda aka ba aikin binciken CBN ya miƙa rahoto ga Tinubu A cewar rahoton Punch, Jim Obazee, wanda ya gudanar da bincike bayan shugaba Bola Tinubu ya naɗa shi, ya gano cewa tun asali ba Buhari ya bada umarnin canza kuɗi ba. A rahoton da ya miƙa, ya ce amincewa da canza takardun N200, N500 da N1000 ya fito ne daga Tunde Sabiu Yusuf, hadimin Buhari, shugaban ƙasa a wancan lokacin.