Dukkanin mu yan Kannywood yan kwankwasiyya ne – inji Dady hikima - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Dukkanin mu yan Kannywood yan kwankwasiyya ne – inji Dady hikima

Dec 26, 2023


Dukkanin mu yan Kannywood yan kwankwasiyya ne – inji Dady hikima


Dady Hikima jim kadan bayan kammala taron addu’oin neman nasarar Abba Gida-Gida a kotun koli, wadda magoya bayan kwankwasiyya na Kannywood suka shirya.


Wanda sanarwa zuwa wajen addu’ar shugaban hukumar tace fina finai na kano abba Al-Mustapha ya fitar sun samu halarta inda kuma jarumi dady hikima yake jawabi ga yan jarida akan wannan muhimmin taro da sunkayi inda ya bayyana hakan kamar yadda gidan rediyon kanawa Radio na wallafa.


“Wannan tafiya ita ake kira da Kannywood Movement kwankwasiyya wannan itace yar kwarya kwarya tafiya ce da anka haɗa domin hadin kai mu yan fim a cikin kwankwasiyya ,daman munsan Allah shi keyi kuma mulki na Allah ne,dukkan wani tsanani akwai sauki a cikinsa, shine muka zo muyi addu’a wannan hali da ake ciki Allah yayi mana maganinsa da masoyan mu na duniya baki daya.- inji Abale.


Shin kuna da kwarin gwiwa?


“Eh muna da kwarin gwiwa, domin kamar yadda na fada mulki Allah ke baiwa wanda yaso koda yana ko ina saboda haka in sha Allah kano ta abba ce, saboda mai duka bashi da sabon aiki tun kafin zuwan ya rubuta me zakayi da lokacin da zaka barshi dan haka muna da kwarin gwiwa bamu da turababi.


Jiya ai kagani duk wani wanda a jihar kano yaga yadda Allah yayi ikonsa saboda haka babu da wani dar Allah ya tabbatar da Alkhairi -inji dady hikima.


Ina kira ga yan uwan mu yan Kannywood kowa dai yasan gaskiya, gaskiya ce yasan karya, karya ce saboda haka a gurin Allah ake nema, mudai munyi addu’a mun barma Allah ikonsa indarabba ba wahala.


Ai ko wane dan kannywood dan kwankwasiyya ne kawai dai za’a tafi neman abinci ne, inda dan kannywood na gaskiya ne to dan kwankwasiyya ne, inda kaga an tafi wani wajen anje ayi tirenin ne a dawo.


Kaso dari cikin ae duk yan kwadan ne sunkaje wani waje kuma sun je domin su amfana, domin bazaka hana dan adam da neman mafita ba.- inji dady hikima.