Ikon Allah - Mace Mai mahaifa biyu ta haifi jarirai biyu Cikin kwana biyu - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Ikon Allah - Mace Mai mahaifa biyu ta haifi jarirai biyu Cikin kwana biyu

Dec 23, 2023


Ikon Allah - Mace Mai mahaifa biyu ta haifi jarirai biyu Cikin kwana biyu


Wata mace mai mahaifa da ba a saba gani ba ta haifi jarirai biyu cikin kwana biyu bayan ta shafe awa 20 tana naƙuda a Amurka.


ATTENTION

For More Update Join Our WhatsApp Group 👇🏻

https://chat.whatsapp.com/GdEk2acGy4X8FFifk2wRtj

Follow Us On Google News 👇🏻

Naijastick On Google News 

Join Our Twitter Group 👇🏻

https://t.me/naijastickfansgroup


Kelsey Hatcher mai shekara 32 ta haifi jaririyar farko ranar Talata, ta haifi ta biyu Laraba asibitin Jamia'r Alabama da ke Birmingham.


Da take bayyana haihuwar jariran da ta kira "ikon Allah" a shafinta na sada zumunta, Ms Hatcher ta yaba wa likitocin a matsayin "masu jajircewa".

Hotuna jarirai guda biyu da aka Haifa a Rana biyu


An bayyana jariran a matsayin 'yan biyu duk da cewa ba ranar haihuwarsu ɗaya ba.


Tun da farko ta zaci za ta haihu ne a Ranar Kirsimeti, amma yanzu ta ce ta koma gida kuma za su yi "bikin ƙarshen shekara a gida".


Tun tana shekara 17 aka shaida mata cewa tana da mahaifa biyu, yanayin da asibitin UAB ya fassara da cewa mata kashi 0.3 ne cikin 100 ke da shi.


Kazalika, asibitin ya ƙara da cewa yiwuwar samun ciki a duka mahaifa biyun ba ta wuce ɗaya cikin miliyan ba.


Likitan da ya karɓi haihuwar tata ya ce "an ɓarke da sowa a ɗakin" lokacin da jaririyar farko ta fito da misalin ƙarfe 7:45 na yammacin yankin a ranar 19 ga watan Disamba.


Sai dai an ciro ta biyun ne ta hanyar tiyata sama da awa 10 bayan ta farko, da misalin ƙarfe 6:10 na safiyar washegari.

(Via)