Jarumin shirin Labarina Abdallah Amdaz “Excellency” zai angwance - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Jarumin shirin Labarina Abdallah Amdaz “Excellency” zai angwance

Dec 26, 2023


Jarumin shirin Labarina Abdallah Amdaz “Excellency” zai angwance


Fitaccen jarumin nan wanda yayi fice a shiri mai dogon zango na shirin labarina wanda kuma mawakin Afrika ne shima zai shiga daga ciki, cikin sanyin nan zai yi wuff da wata.


Abdallah Amdaz yana gayyatar yan uwa da abokan arziki zuwa wajen dauren aurensa kamar yadda ya wallafa katin gayyata a shafinsa na sada zumunta @aamdaz


Ga bayyana da ke cikin katin daurin auren kamar haka:-


Iyalan margayi Abdullahi M. Ammi

Da

Iyalan margayi umar I.timta.


Suna farin cikin gayyatar yan uwa da abokan arziki wajen daurin auren yayansu.


Abdallah Amdaz (Excellency)

Da

Aisha umar timta.


Wanda za’a yi wuri kamar haka:-


Kwanan wata : Assabar 30th December,2023.


Lokaci : 11:00am


Wuri: HRH.Emir of Gwoza Residence Maiduguri opp.maiduguri capital school , Gombole Road, Giwa barracks.


Mutane yan uwa da abokan arziki sunyi farin ciki sosai da fatan alkhairi akan wannan raya sunnah da abdallah Amdaz zaiyi.


A madadin CEO hausaloaded da mabiyanta da ziyarta wannan shafi suna yiwa mawaki kuma jarumi fatan alkhairi, Allah yasa ayi a Sa’a, Allah ya sanya Alkhairi a cikin wannan Aure amen.