Da Zamu dawo muku da Labarin Presido da Sumayya domin bai ƙare ba – Aminu saira - NAIJA STICK

Mobile Menu

Top Ads

More News

logoblog

Da Zamu dawo muku da Labarin Presido da Sumayya domin bai ƙare ba – Aminu saira

Jan 9, 2024


Da Zamu dawo muku da Labarin Presido da Sumayya domin bai ƙare ba – Aminu saira


Daraktan fim din “Labarina” Malam Aminu Saira ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa baya ga labarin Al’amin da Maryam zai sake waiwayar labarin Sumayya da Presido, yana mai cewa akwai abubuwa masu jan hankali da za su faru a cikin shirin nan gaba. Hausaloaded sun tattara wannan bayani kamar haka


Ga yadda firar darakta Aminu Saira da jaridar TRT Afrika sunkayi da shi.


“Abubuwa da yawa muke sa ran zasu faru a shirin labarina, munyi labarin sumayya, yanzu muna yin labarin mai nasara wato al’amin so muna fatan labarai daki-daki zasu biyo shirin labarina kuma masu gamsarwa da ƙayatarwa, in sha Allah.


Ai dama soyayar wahala ce duk wanda kake tunanin ya samu nasara sai ya wahala, kuma shi fim da ake kallo yana kama da gaske ne, shi ya sa za ka ga wani lokaci wani in an yi masa abin da ba daidai ba, za ka ga ya fusata, wani yayi bakaken maganganu.


A koda yaushe musamman fim mai dogon zango akan jima ana yinsa, to daga lokacin da ka kawo karshen matsala idan labari ya kare shi kenan, idan kuma kana bukatar labari ya ci gaba, to dole sai ka sake juya labarin ma’ana idan daɗi ne ake ganin ya zo, to sai a dora a kan wata gaɓar, an saba a kan fim dogon zango kaga ana ta fadi-tashi.-inji Aminu saira.


Amini Saira ya cigaba da cewa a tashi daga wannan matsalar a fada wannan har sai lokacin da anka ce an zo karshe to ba a rufe ba, ga masu kallonmu idan suka duba zasu ga ainihin shi fim din labarina daga sunansa an sa masa labarina ko a baya na sha fada cewa a saurari labarai iri iri ba wai iya labari daya ba .


To labarai ne ake karba na mutane da yawa wannan shine makasudin da ya sa muka sa wa fim din labarina, an samu wata gaba, ta mai ba da wancan labari ta dan tsahirta za ta dan huta, to shi ne aka shiga wani labarin saboda haka labarin sumayya da presido da su raba gardama yana nan bai kare ba.


Kuma muna sa ran in sha Allah za mu dawo kansa, amma yanzu muna kan labarin al’amin mainasara da kuma maryma, jamila da faruk da lawal.


Zuwa shi labarin al’amin da ya kai wata gaba ko ya kai karshe to mu kuma in sha Allahu zamu dawo da labarin sumayya da presido da raba-gardama, duk wanda yace zaiyi harka jama’a to harka ce da za ka hadu da mabanbantan ra’ayi kowa da abinda yake tunani kuma kowa da abinda yake so, wani ka karnata kayi dariya, wani ma dai zai baka haushi, wani kuma kaga a martaninsa akwai abin dauka sai kaga ka dauka -inji Aminu Saira


Muna da tsare tsare wanda muna zaton kwaliya zata biya kuɗin sabulu ,kuma kullum kokarinmu in Allah ya yarda zamuyi iya bakin kokarinmu ga masu kallonmu ba mu kunya ta su ba zamu kawo musu ingantaccen abu-inji aminu saira