Maryam Labarina - ƙalubali ga ƴan mata masu sha’awar shiga harka fim
Labarin kyautar motar da wani bawan Allah Ya baiwa Fatima Hussaini (Maryam Labarina) na fahimci ƙari ne kan ƙalubalen da ƴan mata ke fuskanta na kwaɗayin shiga harka Fim don neman suna ko samun abin duniya. Matsala ce da ka iya kai wa ga wasu cikin matan aure (masu kwaɗayi) su kashe aurensu domin su gwada ta su sa'ar.
Kai hatta abokan sana'a a Fim ɗin ƙalubale ne garesu domin ko da a ce ta jima a Indostirin to tauraruwarta bata fara haskawa ba sai a shirin Fim ɗin Labarina da ta fara fitowa a ƙasa da watanni biyu. Wanda anan ta tarar da tarin matasa, dattawan mata da maza waɗanda a wasu lokutan sai sun yi da gaske wajen jure wulaƙanci da ƙasƙanci kafin a saka su a Fim ɗin da za a sallame su da kuɗin da ba su wuce Naira dubu 5 zuwa 10 ba.
A gefe guda ga tarin waɗanda lalurar rashin lafiya ta kwantar, suna fama da neman na magani, babu cin yau ballantana na gobe. Waɗanda a ganina su ya kamata a ce ana taimakawa duba da gudanarwar da suka jima suna bayarwa.
Idan kuma kana magana ta burgewa ko tausayawa ga role ɗin da Tauraro ya hau a Fim ne to ina ka bar irin su Malam Kamaye na shirin 'Daɗin Kowa?' wanda kamata ya yi a ce yanzu ya rasa idan zai saka kyauta daga masu kallo.
Kai a ma jingine taurari a gefe, ina ka bar Marubuta, Furodusas da Daraktoci?
Shin ba su ne ababan burgewa a matakin farko ba?
Ita ma Maryam ɗin da kamata ya yi a ce ta boye labarin kyautar motar da aka yi mata ko don gudun baki da abin da ka je ya zo.
Allah Ya sa mu dace, Ameen Ya Hayyu Ya Ƙayyum.