Nayi farinjini da banyi zato ba duk akan shirin Labarina – Sadiq sani sadiq - NAIJA STICK

Mobile Menu

Top Ads

More News

logoblog

Nayi farinjini da banyi zato ba duk akan shirin Labarina – Sadiq sani sadiq

Jan 20, 2024


Nayi farinjini da banyi zato ba duk akan shirin Labarina – Sadiq sani sadiq


Shahararren jarumin nan SadiQ sani SadiQ a cikin wata fira da gidan jaridar TRTAFRIKA Hausa sun kayi da shi akan shirin labarina mai dogon zango wanda yanzu haka ake haskawa a tashar YouTube da kuma arewa24tv.


Al’amin mainasara wanda shine sunan sa a shirin labarina ya bayyana cewa tabbas tskanin jamila da maryam ko wace yaji daɗin aiki da su duba da yadda ko wace ta taka rawa akan matsayin da anka bata.


Bugu da ƙari ita maryam ba wannan ne karfon farko da sunka fara aiki da ita ba amma duk sun yi kokari sosai harda kakarawa naji dadin aiki da su sosai.


Daukar da na fi so a cikin shirin labarina


A lokacin da iyalina sunka mutu nazo asibiti naga gawawarkin yana yin da na shiga hatta wadanda suke kallo da ma’aikatan kowa sai da ya tausayamin a wannan lokacin gaskiya nafison daukar fiye da ko ina.


Gaskiya a rayuwata ban taba daukar waya sosai akan shirin fim ba kamar labarina domin wasu sukan manta sa suna na sadiq sani sadiq suna kirana da al’amin ko mainasara.


Sakon da nake baiwa masoya shine akwai abubuwa sosai a cikin shirin labarina sosai wanda yanzu ma anka fara akwai nishadi sosai wanda kamar yanzu ma anka fara shirin labarina.


(Via)