Sababbin Finafinan Kannywood Da Za A Fara A Bana
finafinan da suka yi shuhura a bara, a bana tuni masu shirya finafinai da dama sun shirya tsaf domin kawo sababbin finafinan.
Yanzu za a iya cewa masana’antar ta fara dawowa da karfinta, kasancewar an fara yin sababbin finafinai a Kaduna da Jos, bayan na Kano da sauran jihohi.
Daga cikin sababbin finafinan da za a fara a bana akwai:
Zafin Nema
Zafin Nema fim ne na Abdul Amart Maikwashewa, wanda ya tsara bayan nasarar da ya samu a fim din Manyan Mata, sannan a wannan karon ba kamar yadda aka saba ba, Yaseen Auwal ne ya ba da umarni ba Sadik N. Mafia ba.
A fim din akwai jarumai irin su Maryam Yahaya da Mommee Gombe da Sadik Sani Sadik da sauransu.
Darasi
Darasi fim ne da aka yi a Jos, karkashin Kamfanin 3SP International, wanda ya shirya wakokin Sambisa da sauransu.
Akwai jarumai irin su Ali Nuhu da Mommee Gombe da Shamsu Daniya da sauransu.
Fim din ya fara tashe ne tun kafin a fara haska shi a lokacin da wasu a kafafen sadarwa suka yi ca a kan jaruma Mommee Gombe ta sanya kayan NYSC.
Alhaji Isma’il ne ya dauki nauyi, sannan daraktan kamfanin 3SP, Abubakar S. Shehu ya ba da umarni.
Sauran sun hada da Zainabu na Yusuf Dan Mana da A cikin biyu na Aishatu Humaira da Al’ummata na Sani Candy da sauransu da duk za a fara haskawa a bana.