Allah yayiwa jaruma Bintu ta dadinkowa rasuwa yau Lahadi
Babbar jarumar nan ta shirin nan naku Mai dogon zango wato shirin Dadin kowa Wanda tashar Arewa 24 take haskawa akowace ranar Asabar ta karshen mako.
Kamar yadda shafin BBC Hausa suka bayyana cewa :
Ƴan uwan jarumar fim ɗin sun bayyana wa BBC cewa ta rasu ne ranar Lahadi bayan fama da jinya.
Tuni dai aka yi jana'izarta a unguwar Gunduwawa da ke Kano, kuma abokan sana'arta na ci gaba da jimamin rashinta.
Allah yajikanta da rahama yagafarta Mata zunubanta.