Hotuna ramar hadiza Gabon ya jawo cece kuce
Jaruma hadiza aliyu garbon ta wallafa wani hotunta wanda ta rame da yake jawo a shafukan sada zumunta, ya jawo cece kuce sosai.
Hadiza gabon ita da kanta tasan da cewa sai mutane sun tofa albarkacin bakinsu irin yadda anka sanya ta cika kamar leda, amma kwatsam sai ga wani hotun ta, ta koma wata irin shamu shalle.
Hadiza gabon ta wallafa hotunan a shafinta inda mutane sunka tofa albarkacin bakinsu su, ta magantu akan wannan hoto.
Hausaloaded ya tattaro martanin da mutane sunkayi mata a karkashin wannan fustin.
@muazurahama cewa take yi : Allah ka rabamu da ciwon rama amma Maganar gaskiya kinfi kyau kina yar duma dumanki hajiyata.
@beauty_by_rauda_skincare ga abinda take cewa : @muazurahama wlh kuwa kaman batada lfy saiya fito mata tsofan ta gaba daya wlh duk wanda yabata wanann shiwaran baiyi ba.
@bridal_boutique96 cewa suke : Nidai dan Allah ki fadamun abunda kika sha kika rage kibar nan, But gaskiya a hotunnan kamar bakida lafiya.
@isahahmadrufai cewa yake yi : Indai haka sliming yake maida mutum yakoma kalar tausayi kamar Wanda yatashi daga jiya to babuni Babu sliming har abada.
@fsi_collection_and_sent cewa suke yi: Gaskiya Abun kuma yayi yawa ,mu masoyan ki kına ja mana magana pls ki tsaya haka nan ramar tayi yawa.
@dr_basira_dantata : tana mai fadin cewa : Ina so zan baki shawara baki masifa ne ki guji abinda mutane zasuyi ta tankaki a duk lokacin da zakiyi posting Ki rubuta tabarakallah mashaAllah a qalla duk wand ze ga posting din shima ze karanta amma maganar gaskiya akwai hadari ki dinga dora pics don ayi magana ana tanka ki baa cewa tabarakallah kuma baki san bakin wasu ba take care @adizatou.
@queenmoofy cewa take: Kun taba zama kun tambayeta dalilin slimming nata?Sai dai kawai kuta ranting.Kinyi kyau abunki dije