Jaruma Hannatu bashir tayiwa Adam a zango raddi akan maganarsa ta ƴan matan kannywood
Shafin Hausaloaded sun ruwaito cewa - Fitaccen jarumi adam a zango yayi wata zantawa da wallkiliyar BBC Hausa safiya maishanu a cikin shirin mahangar zamani inda anka tattauna da shi akan wasu abubuwa akan rayuwarsa da kuma masana’atar sa.
Inda yake cewa kashi tamamin cikin dari mata da suke harka fim a kannywood ba da son iyayen su ba sun fi karfinsu wanda maganar ta dauki hankalin mutane domin cewa sune masu bada umurni ko shirya fina finai, kuma yana daga cikin manyan jaruman masana’atar Kannywood amma yana daɓawa kansu wuka.
Domin irin wannan kalamai yakamata aji su daga wajen yan wajen gida ba irin yan cikin gida ba wanda ko a kwanaki a wata fira da ankayi da Nazir dan hajiya shima yayi irin wannan cewa shi bai san inda yan matan kannywood ke samun kuɗi ba.
Shine daya daga cikin masu shirya fina finai kuma jaruma hannatu bashir tayi wani bidiyo a shafin tiktok dinsa @hannatubashir tayi bidiyo inda take yimusu martani akan wannan kalamai.
“Bayan sallama irin ta Addini musulunci ina da wani tsokaci da zanyi akan kullum cikin hira muke da manema labarai amma wani sa’in akwai kura kurai a ciki musan abinda zamu fada musan abinda zamu fadawa, mu rinka yiwa junan mu adalci baki daya.
Idan anyi fira da wani kalma sai ta ɓata kowa , ta jawa kowa baƙin jini, zagi ko bakar magana, naji wani yana cewa matan kannywood da ke shigowa sun fi karfin iyayensu , iyayen su basu isa da su ba, wannan kuskure ne a cikin magana ya kamata musan me muke fada , mu rinka yiwa junan mu adalci.
Wallahi ban fi karfin iyayena ba , har yanzu iyayena suke fadamin abinda suke so inji, kuma shi nake ji ba wata mace da ake cewa tafi karfen iyayenta ne tazo kannywood, ba wanda zai sanya ta taji wannan ba furuci bane .
Sa’a nan da kake cewa ta baro gidan su tafi karfin gidan su ne ta shigo fim , to wannan furucin ana so ace fim ba sana’a bace? Idan ba sana’a bace wanda yake furucin hakan miyasa yake yin ta, in ba sana’a bace, dan Allah mu ringa yiwa junan mu adalci.
Mu mata kullum mu kuke jawowa bakin jini na wasu maganganu wanda baku yi mana adalci kuna dorawa akan mu,kuma duniya ta kallemu da su tana zagin mu, mu matana fah muna so muyi aure kuma zamu haifi ‘ya’ya kuna so ku barma yayan mu wani abu da za’a kalle su ace ga abinda iyayen su sunkayi, kuma wani ne yake fada bamu bane keyi.
Ta ina ƴa zata fito ace tafi karfin iyayen ta, to idan ta baro gidan ta zo fim, shin shi fim din ba sana’a bace amsar da nake na samu kenan, kuma wanda yake fadin haka bai dace yayi fim din ba”- inji hannatu bashir.