Sanarwa akan Shirin Labarina season 8 – Aminu Saira - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Sanarwa akan Shirin Labarina season 8 – Aminu Saira

Feb 22, 2024


Sanarwa akan Shirin Labarina season 8 – Aminu Saira


Fitaccen mai bada umurni Aminu saira wanda shine ke shirya fim din labarina mai dogon zango wanda yanzu haka ake cikin zango na takwas, inda labarin ya dau zafi.


Yanzu ana kan labarin al’amin mainasara da maryam akan labarin irin yadda mutuwar matarsa zainab ta sanya shi ya shiga wani yanayi a cikin shirin har anka samu wata tazo aurensa amma tayi ne domin ta kashe shi, ta mallaki dukiyarsa.


Shine mai bada umurni malam aminu saira yake bada wata sanarwa akan shirin labarina inda yake cewa.


“Ina da wata taƙaitaciyyar sanarwa mun so ace wannan sati ranar juma’a mu sanya karshen zango na takwas 8 ‘season 8’ a arewa 24 zai kasance a awa biyu , a youtube channel zai kasance awa biyu 2, sakamakon bamu samu dai-dai tu na time din daya ba, na youtube zamu sanya awa biyu shine zai zamo kashen zango na takwas 8.


Shi kuma na arewa 24 zai kasance na awa daya , wannan sati sai kuma wani satin mu sanya awa daya, saboda haka masu biyarmu a youtube zasu kalli cikakken karshen zango na takwas 8. Sai kuma ga waɗanda suke bibiyar a arewa 24 zai kasance sati biyu.


Saboda haka muna bada hakuri ga masu bibiyar ga a arewa 24 , mun so mu hada shi awa biyu amma bamu samu a hade ba, saboda haka duk mai son kallon karshen season 8, dole ya garzaya a youtube channel.


Muna godiya ga jinjina ga masu bibiyar mu, mun gode muna muku fatan alkhairi,muna ban gajiya Wasallamu alaikum warahamatullah.-inji saira movies.