Sheikh Pantami ya gwangwaje dalibar da ta lashe gasar musabaƙa da kyautar mota da tallafin karatu
Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya gwangwaje dalibar da ta yi nasara a gasar musabaka ta duniya da kyaututtuka.
Pantami ya bai wa dalibar mai suna Hajara Ibrahim Dan’azumi kyautar mota da kuma tallafin karatu har ta kammala.legit na ruwaito.
Martanin Hajara kan wannan kyauta
A cewarta:
“Da farko ina yi wa Allah godiya da ya ba ni wannan nasara saboda addu’ar da muke yi ne ta yi tasiri.
“Ina kuma mika godiya ga iyaye na da suka tsaya tsayin daka suka ba ni tarbiyya har na kai ga wannan nasara.
Hajara ta kara da cewa:
“Tabbas tsohon Ministan ya neme mu jiya har ya ba ni kyautar mota kuma ya ce har in kammala makaranta zai biya min.
“Na ji mai girma Gwamna ma ya ce idan ya dawo zai kirani, ina fatan Allah ya dawo da shi lafiya ya sanya alkairi a duk abin da zai faru.”
Daliba ta lashe gasar musabaka ta duniya
Kun ji cewa wata daliba daga jihar Gombe ta yi nasarar lashe gasar musabaka ta duniya da aka yi a kasar Jordan.
Dalibar mai suna Hajara Ibrahim Dan’azumi daga unguwar Tudun Wada ta yi godiya ga Ubangiji kan wanna nasara.
- Hausaloaded