Talaka na daf da yiwa Gwamanti tawaye, mun gaji da basu hakuri – Mai martaba sarkin musulmi
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya Gargaɗi gwamnatin Najeriya ta gaggauta ɗaukar matakin sauƙaƙa wa talakawa rayuwa da fatattakar yunwa, matukar ba haka ba kuma ta kuka da kanta kan matakin da talakawan zasu ɗauka a kanta,majiyarmu ta samu wannan labari daga shafin dokin karfe tv
Da ya ke yiwa manema labarai jawabi a Arewa House da ke jihar Kaduna, Sarkin musulmin yace Sarakunan gargajiya dana shugabannin addini sun gaji da tausar talakawa da kuma basu haƙuri, don haka babu makawa illa gwamnati ta ɗauki matakin sauƙaƙa rayuwa.
Ya ce a yanzu talakawa sun kai geji kuma tura ta kai bango kana Sarakunan gargajiya ba zasu iya tare talakawa ba idan suka fusata da gwamnati.
Ya ce kullum maganar kenan da gwamnati ke yi musu kan suci gaba da tausar talakawa, har zuwa yaushe ne za’a ci gaba da bada hakuri? Har zuwa yaushe ne talakawa zasu ci gaba da mutuwa da yunwa da sunan haƙuri? A yanzu lokaci ne da gwamnati zata yi haƙuri ta ɗauki matakin da ya dace.
“Mun jima muna roƙon talakawa, a yanzu mun gaji, kunyar su muke ji, sun fara daina yarda da maganar mu, don babu wata alamar sauƙi daga gwamnati don haka matuƙar gwamnati bata dawo cikin hayyacin ta ba, to duk matakin da talakawa suka ɗauka tabbas ta kuka da kanta” inji Sarki Musulmi.