Yarinyar da ta haihu tana da shekara 5 a duniya - NAIJA STICK

Mobile Menu

Top Ads

More News

logoblog

Yarinyar da ta haihu tana da shekara 5 a duniya

Feb 6, 2024


Yarinyar da ta haihu tana da shekara 5 a duniya


Wannan labarin wata yarinya ne mai suna lina medina wadda ta kare tarihi “Guinness World record ” wanda nima wannan labarin da nake rubuta muku labarin ya bani mamaki wanda a tarihin hausaloaded wannan shine labari mafi ɗaukar hankalin mu, kamar yadda abisfulani ya labarto mana, uniland ta ruwaito.


Wannan lina medina itace yarinya da ta samu juna biyu tana yar shekara 5 kuma ta haifeshi ga ta nan dauke da jaririn ta.


Taya abun ya faru?


Wanann yarinya itace mahaifiya ta farko a duk duniya ta haihu da ƙanan shekaru kamar yadda kuke gani sunan ta lina medina yar asalin kasar peru ce da ke kasar South America, da farko dai babu wanda ya fahimci yarinyar nan lina juna biyu ne dauke da ita, suna zaune a wani kyauye mai suna andes, kawai sai anka ga cikinta ya fara girma.


Da anka ga cikin yarinya yana kumbura kowa na fadin albarkacin bakinsa cewa ciwon kaza ne ciwon kaza ne, har mahaifiyar yarinyar nan ta gaji ta dauke ta sunka garzaya a asibiti, a nan anka fahimci fa lina tana dauke da juya biyu na bakwai bakwai, wata sabuwa, a nan fa hankalin mahaifiyarta ya tashi , domin itama abun ya zamo abin al’ajabi ace dan shekara biyar da ciki.


Daga baya dai anka ciro namiji daga lina, anka gano cewa akwai ciwon da balaga tana zuwa wa ƙananan yara , domin ta fara jinin al’ada tun tana yar shekara ukku kacal a duniya.


Shin waye yayiwa Lina Medina ciki?

 

Ita dai lina bata da wayo da zata iya fadin wanda yayi mata ciki, amma daga baya anka kama mahaifiya ta, amma daga baya an rasa samun hujja ta tattabar da shi din ne anka sake shi yayi tafiyarsa..


Yaya ɗan lina ya taso tare da mahaifiyar sa .


Shi dai yaron ya taso yana yiwa lina kallon yayarsa domin shekara biyar ne tsakanin su bata iya kula da shi, da yakai shekara goma anka gayamasa ita ce mahaifiyarsa bai yarda ba, sai daga baya da yaji abinda ya faru sa’a nan ya yarda.