Aminu J Town ya baiwa Hukumar hisbah kyautar mota
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce wasu ƴan Tiktok sun gwangwaje ta da kyautar mota don ci gaba da ayyukanta na “Operation Kau da Baɗala”.
A bidiyon da Hisbah ta wallafa a shafinta na Facebook, an ga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da mataimakinsa Dr Mujahid Aminuddend suna karɓar kyautar daga hannun ɗaya daga cikin ƴan Tiktok ɗin, Aminu J Town, wanda shi ya kai motar ƙirar Toyota takanas tun daga Jos.
Wannan lamari na zuwa ne kwana guda da komawar Sheikh Daurawa ofishinsa sakamakon sasanta su da aka aka yi da Gwamna Abba K Yusuf, bayan saɓanin da suka samu a wancan makon.
Kwamandan hisbah tare da mataimakinsa sun karbi motar daga aminu j town daga abokansa inda yake cewa.
“Alhamdullahi muna karba mota a karkashin operation kauda badala daga wani dan tiktok aminu j town gudunmawa tare da wannan kungiyar tasu , wadanda suke fafatawa tiktok sunka ga ya dace su bada guduwa tsaftace da gyaran tarbiyya al’umma a wannan jiha ta mu, da ma na Nijeriya baki daya.
Muna rokon Allah ya saka da alkhairi kuma a cigaba da kawo muna wannan tallafi da gudumuwa a chi gaba da bawa hisbah guduwa wajen tsaftace al’umma da gyaran tarbiyya muna muku godiya kuma muna mufatan alkhairi , Allah yasa albarka”- inji kwamandan hisbah sheikh aminu Ibrahim daurawa.
Kalli bidiyon anan: