Mai POS Ya Maida N10m Bayan Kwastomansa Ya Tafka Kuskure, Ya Samu Kyauta
Kuskuren tura Naira miliyan 10 a POS Hakan ya faru ne yayin da kwastoman ke kokarin tura N10,000 amma ya yi kuskuren tura miliyan 10.
Rundunar 'yan sanda ta bayyana haka ne ta bakin kakakinta, Abdullahi Haruna Kiyawa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis 14 ga watan Maris. Kiyawa ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a watan Disambar shekarar 2023 lokacin da mai sana’ar POS, Mohammed Sani Abdulrahman ya kawo rahoto ofishinsu. Ya ce Abdulrahman ya fahimci kwastomansa ya yi kuskuren tura masa Naira miliyan 10 madadin N10,000. Daga nan ne rundunar ta karbi bayanan abin da ya faru tare da fara gudanar da bincike domin tabbatar an samu mai shi.
Rundunar ta ce ta shafe watanni uku ta na bincike kafin ta gano mai kudin wanda ɗan kasuwa ne a Kasuwar Dawanau da ke Kano.
Gaskiya ta bayyana Kiyawa ya ce mai POS ya mayarwa mai kudin hakkinsa inda ya ba mai POS ɗin kyautar N500,000. Har ila yau, rundunar 'yan sandan ta yaba da kyakkyawan halin da mai POS din ya nuna kuma ta shawarci sauran jama’a da su yi koyi da shi.
Wannan ma zuwa ne bayan wani mai adaidaita sahu ya mayar da miliyan 15 ga wani kwastoman dan kasar Chadi a Kano.