Ni ne gimshiƙin zaman Ali Nuhu MD a ƙarƙashin gwamtin Tinubu da na kafa – Dauda Kahuta Rarara
Fitaccen mawakin siyasa Dauda Rarara ya bayyana cewa a sana’ar waƙa a Najeriya ya zarce kowa.
Rarara ya bayyana haka a lokacin da yake hira da jaridar TRT da ta buga a shafinta ranar Lahadi
A hirar Rarara ya yi ikirarin cewa shi ne ya fi kowa rera wakar siyasa a Najeriya kuma dole ake biyo shi har inda ya ke don ya yi waka
Da aka tambayeshi game da mukamin da gwamnatin Tinubu ta yi wa Ali Nuhu, Rarara ya ce shine ginshiƙin zaman Ali Nuhu MD a masana’antar fim n ƙasa.
Ni na kafa gwamnatin Tinubu, kuma na ji daɗin muƙamin da aka naɗa Ali Nuhu akai, saboda haka ina farinciki matuka, amma ba a wai an saka min bane tukunna.
Idan ba a manta ba Rarara ya ce shine ya kafa gwamnatin Tinubu, kuma ya kamata a bashi akalla kujerun minista biyu ya raba sannan a saka shi cikin ƴan gaban goshin gwqmnatin Tinubu da za su rika gudabar da mulki a yanzu
A baya dai Rarara ya yi fice ne wajen rera wa tsohon shugaban Kasa Buhari waƙa, sai dai kuma tun bayan kammala mulkin Buhari, Rarara ya raba jiha da Buhari, inda ya caccaki mulkin sa ya kuma yi Allah Wadai da salon mulkin sa.
~ Premium Times Hausa