Ni zan zamewa adam A. zango matar mutukaraba idan har ya yarda zai aure ni, cewar ruƙayya abdurrahman - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Ni zan zamewa adam A. zango matar mutukaraba idan har ya yarda zai aure ni, cewar ruƙayya abdurrahman

Apr 16, 2024


Ni zan zamewa adam A. zango matar mutukaraba idan har ya yarda zai aure ni, cewar ruƙayya abdurrahman 


Duba Wannan Labari >>> Muhimmiyar sanarwa akan Labarina Season 9 – Aminu Saira


Biyo bayan matsalar rashin dacen aure da fitaccen jarumin masana'antar Kannywood Adam A. Zamgo ke fuskanta, wata tsaleliyar budurwa ƴar asalin ƙasar Nijer, Ruƙayya Abdurrahman ta bayyana cewa a shirye take ta kawo ƙarshen hawayen dake kwaranya a zuciyar Adamun.


Ruƙayya ta bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da tayi da Jaridar Dokin Karfe TV a wannan rana kamar yadda ta ce: 


"Mutane suna zargin Adam A. Zango da auri saki ko auren ɗanɗano, amma bisa kalaman da yayi a jiya na fahimce shi, matsalar ba daga gare shi ba ne dacen mace tagari ne bai yi ba, dan haka ni zan zame masa matar mutukaraba idan har ya yarda zai aure ni". In ji ta.