Ɗaliba Ta Maka Makarantarsu Kotu, Ta Nemi Diyyar Miliyan ₦505 Kan Cin Zarafin ta - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Ɗaliba Ta Maka Makarantarsu Kotu, Ta Nemi Diyyar Miliyan ₦505 Kan Cin Zarafin ta

May 14, 2024


Ɗaliba Ta Maka Makarantarsu Kotu, Ta Nemi Diyyar Miliyan ₦505 Kan Cin Zarafin ta


Wata ɗalibar makarantar ‘Lead British International School’ da ke Gwarimpa a Abuja mai suna Namitra Bwala, ta kai ƙarar makarantarsu tare da neman a biya ta diyyar zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan ₦505 sakamakon laifin cin zali da cin zarafin da aka yi mata.


Idan ba a manta ba LEADERSHIP HAUSA ta rawaito yadda lamarin ya afku bayan da wani faifan bidiyo ya watsu a shafukan sada zumunta wanda a bidiyon aka ga yadda wata ɗaliba mai suna Mariam Hassan take cin zalin Namtira Bwala, bidiyon dai ya janyo cece-ku-ce a kafafen sada zumunta, wanda hakan ya sa mutane da kungiyoyi suka yi tir da kuma kiran a yi mata adalci.


Bayan faruwar hakan, mahukuntan makarantar sun fitar da wata sanarwa domin kwantar da hankula wacce take nuna za su yi bincike kan al’amarin.


Daga cikin waɗanda suka sanya baki a maganar har da ma’aikatar harkokin mata da kuma wacce ta aikata laifin wato Maryam inda ta fitar da wani bidiyon na bayar da haƙuri tare da neman afuwa.


Amma da alama wannan bai sanya iyalan Namitra Bwala su yafe ba. Domin kuwa a safiyar yau Litinin ne, Mista Daniel Madu Bwala, wanda yake a madadin mahaifinta ya shigar da makarantar ‘Lead British International School’ ƙara a wata babbar kotu da ke birnin tarayya Abuja bisa zarginsu da yin sakaci da rufa-rufar abinda ya faru.


Kamfanin lauya mai wakiltar Namtira, Deji Adeyanju and Partners, sun bayyana cewa wanda suke wakiltar na son kotun ta tilastawa makarantar biyansu Naira miliyan ₦500m kuɗin diyya da kuma Naira miliyan biyar kuɗin da suka kashe wajen shari’a saboda sakacin makarantar na rashin ɗaukar matakan da ya dace kamar yadda doka ta tanada.


Bayan makarantar ta biya waɗannan miliyoyin kuɗaɗen, iyalan ɗalibar da aka muzanta na son a rubuta wasiƙar bayar da haƙuri gare su wacce dole sai an wallafa ta a manyan jaridu biyu na Nijeriya.


Lead British international school Namitra Bwala