Gaskiyar Zance Akan hadarin motar da jaruma Maryam wazeeri sukayi ita da mijinta
Tsohuwar Jarumar Fim, Maryam Waziri wacce aka fi sani da Layla a cikin Shirin Labarina sunyi hatsarin mota tare da mijinta tsohon ɗan wasan ƙwallon Super Eagles na Najeriya, Tijjani Babangida, da ɗansu.
A Yau ta ruwaito iyalan sun yi hatsarin ne akan hanyar Kaduna zuwa Zaria kuma anan take ƙanin Tijjani wato Ibrahim Babangida ya rasu a yayinda aka kwashi Maryam da mijinta da yaronta zuwa asibiti.