Halin Da Mata Ke Shiga Sakamakon Rashin Samun Gamsuwa Daga Mazajensu
Akwai mata da dama masu fuskantar matsaloli na rashin samun gamsuwar jima’i daga wajen mazajensu a wannan zamani da ba su iya fada musu, wanda hakan ke kara jefa su cikin damuwa.
Wasu matan na tsintar kansu wajen bin mazajen banza a waje, sakamakon rashin samun cikakkiyar gamsuwa daga wurin mazajen nasu, duk da dai bai kamata wannan ya zama hujja ta yin masha’a ba.
Ya kamata a lura da cewa, duk irin jaraba ko karfin sha’awar da mace ke da ita; idan har namiji na iya gamsar da ita yadda ya kamata, ba za ta taba daga kai ta kalli wani namijin daban ba.
Amma shi kuwa namiji, duk yadda kika kai da iya gamsar da shi ko sanya shi nishadi; da zarar ya hango wata daban kuma sai dai kawai wanda Allah ya tsare. Har ila yau, matsalar da ke faruwa a wannan lokaci; musamman ganin yadda matan aure ke bin maza a waje, ya samo asali ne daga wadannan abubuwa da za a zayyano kamar haka:
1- Rashin samun cikakkiyar gamsuwa daga wajen namiji, in har mace za ta ci ta sha ta koshi, sannan hankalinta a kwance; ai kuwa wajibi ne ta bukaci da namiji a kusa da ita.
Hakika bincike ya tabbatar da cewa, ‘ya’ya mata sun fi maza karfin sha’awa, domin kuwa idan har mace na da lafiya; dole ne ta bukaci namiji, sannan ba kowace mace ce ke iya mallakar kanta ba; musamman idan bukatar da namiji ta bijiro mata, shi yasa wasu suke kai wa ga fadawa ga halaka.
Amma, mafi yawan lokuta idan muka duba; za mu tarar da cewa laifin mazan ne; domin kuwa idan har namiji zai biya wa matarsa bukata, ko kadan ba za ta taba kallon wani namijin daban ba.
Mene ne ke hana wasu matan samun gamsuwa daga mazajensu?
Rashin cikakkiyar lafiya daga wajen da namiji, kamar matsalar sanyi, basir, hawan jini, ciwon siga, rashin abinci mai gina jiki ko matsalar istimna’i da sauran cututtuka da ka iya taba lafiyar al’aurar da namiji.
– Tana iya yiwuwa kuma matsalar daga wajen macen ne, kamar matsalar da suke fama da ita ta sanyi (infection), wanda ke hana su samun gamsuwa ko jin dadin saduwa da miji ko kuma matsalar iska, wato namijin dare (Aljanin da yake aurar mace), sai ya hana ta jin dadin saduwa da mijinta kwata-kwata.
2- Rashin kwarewa wajen tarawa da matarka tare kuma da rashin cikakken ilimin yadda za ka sarrafa ta, ta yadda za ta samu gamsuwa tare da nishadi daga wurinka.
3- Son kai daga bangaren da namiji: kusan kaso 9 cikin 10 na maza, na da matukar son kawunansu ta wajen biya wa kansu bukatar aure. Domin kuwa, da zarar tasu bukatar ta biya; babu ruwansu kuma da bukatar ‘ya mace.
Saboda haka, ya zama wajibi mu kula da matanmu tare da kokarin sauke nauyinsu da ke kanmu, domin tseratar da su daga fada wa irin wannan mummunan hali ko halaka, wato bin wasu mazajen a waje.
#hausaloaded.com