Munyi nadamar tsayama murja a kotu – lauyoyin murja kunya
Lauyoyin da ke kariyar murja kunya a shari’ar da hukumar hisbah na kai ƙarar shahararriyar yar tiktko labarin da ya dauki hankalin mutane a nahiyar afrika kan cewa ankai ta gidan yari ta tsire.
Lauyoyin sun bayyana cewa guiwoyin su sunyi sanyi a lokacin da sunka ga faya fayan bidiyo da sababbin hotuna da jarumar ta bayyana a kafar sada zumunta wanda yana daga cikin sharuddan beli cewa an haramta mata aiki da kafar sada zumunta har sai an kammala shari’a.
Kwatsam yan kwana kin nan sai ga sababbin bidiyo da hotuna suna yawo na murja kunya bayan ba’a kamala sharia ba, kamar yadda majiyarmu ta freedom radio kano na samu zan tawa da su.
A cikin bidiyon da murja na saki harda wata waka mai ciki da zambo da habaichi da zaku ji a wannan bidiyo tana sitidiyo.
https://hausaloaded.com/2024/05/munyi-nadamar-tsayama-murja-a-kotu-lauyoyin-murja-kunya.html?fbclid=IwZXh0bgNhZW0CMTEAAR2f6D4WjkrxOc1o694Z_u-pbIZGroNL6z6LFZZVPyGO4Em_oHFBGazFwbM_aem_AXZQpRCk_36PmVjm9UrxfuYiMUt6qDP9FrvSRC9akv1_BP5fBuaWGXMf8QkWTGojdHBIm5ugIsCTqVkUq5y-J_L1
Ga abinda lauyanta ke cewa zan tawarsa da manema labarai
“Abun takaici ne sosai , abin ban haushi , mun dauki dukkanin kalubali wanda a cikin mu bamu taɓa fuskantar iri wannan kalubali a dukkan shekarun aikin mu na lauyoyi, kuma bamuyi murna da wannan ba, guiwoyin mu sun sare.
Mun ji wani abu na danasani wanda kuma a kansa muke har yanzu , wannan yanayi abun da nasani ne sosai sosai dole ne a girmama umurni kotu” – inji barista Au hajj
Kotun da ta bayar da belin murja kunya wanda baba jibo Ibrahim kakakin kotu jiha sun bayar da umurni da a kamota.
“Wannan umurni ne da anka baiwa Kwamishinan yan sanda na jihar kano cewa idan ta saɓa to ya kamota ya bayyanar da ita a gaban kotu, saboda kotu ta bashi daman akan sharudan da anka sanya idan ta saɓa ya kamota, saboda haka muna kira da ya bi umurnin kotu tare da hujjoji na ta aikata abin anka ce karta sake aikatawa.- inji kakakin kotu kenan.
A ɓangaren rundunar yan sanda jihar kano tace ta tabbatar da umurnin kotu kuma zasu duba yiyuwar matakin da ya dace kamar yadda kakakin rundunar yan sanda haruna abdulllahi kiyawa ya bayyana.