Na yafewa G fresh lefe da sadaki idan ya amince da soyayya ta – Hajiya Khadija - NAIJA STICK

Mobile Menu

يتم التشغيل بواسطة Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Na yafewa G fresh lefe da sadaki idan ya amince da soyayya ta – Hajiya Khadija

17‏/05‏/2024

Na yafewa G fresh lefe da sadaki idan ya amince da soyayya ta – Hajiya Khadija


Wata ma’abuciya mai harka manhajar titkok hajiya khadija wadda anka fi sani da lady asiwaju amma a can baya ita yanzu ba tashi bace, ta bayyana irin soyayyar da take yiwa Al’ameen G-fresh Kano state materials.


A zantawar da freedom radio kano ta bayyana cewa idai G-fresh ya amince da soyayar ta to ta yafe masa sadaki da lefe kuma a gidan ta zasu zauna.


Al’ameen G-fresh mutum ne wanda yayi suna a manhajar titkok kuma dan madubin mata ne a kafar tiktok tun bayan auren su da sadiya haruna anka samuɓ matsala wasu matan na fara nuna irin so da suke masa ashe sadiya ta riga su ne tayi wuff da kayanta kafin a rabu.


Na dade ina son G-fresh zuciyata ta Kamu da son shi tun farkon rade radin auren shi da naji na dauka wasa ne, sai ban damu ba har ango nayi amma ban samu naje ba.


Naje kano amma na kasa zuwa saboda zuciyata bazata jure ana daurawa masoyina aure ba, indai zai amince ni gidan da zamu zauna banda matsala, lefenshi na yafe ni zan masa, kuma ni zan bada sadakina na bashi ya bada“-inji hajiiya khadija.


Saurari saura bayyani ga faifan bidiyo nan.