Gwamnonin arewa maso yammacin kasar nan na gudanar da taro kan inganta tsaro a Katsina.
Hukumar raya ƙasashe ta majalisar dinkin duniya ke shirya taron wanda ake fatan fito da hanyoyin da za a kawo karshen matsalar tsaro a yankin.
Cikin masu halartar taron har da mataimakin shugaban kasa Khashim Shatima da manyan jami’an tsaro da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Taron na kwana biyu na da nufin inganta tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya kuma zai mayar da hankali ne, wajen samun hadin gwiwar gwamnatocin yankin don tsare al’umma da sana’o’i.