Ni Na Yi Silar Da Rahma Sadau Ta Rabawa Jama’a Kudi, Amma Ni Ko Kobo Ban Samu Ba – Idris Bello
A ranar juma’a da ta gabata jarumar ta sanarwa a shafinta cewa zata rabawa mutane kudi ga wanda Allah yasa yana daga cikin masu nasara da zata dauki asusun bankin su.
Wanda duban mutane sunka aje asusun bankin su wanda ta baiwa mutum 100 domin rage radadin talauchi, shine wani matashi da shine ya nema ta taimakasa tace ya tura asusun bankin sa amma shiru ya tashi tsu la babu ko sisi kamar yadda ya bayyana.
“Ni Idriss Bello Danchuwa nine mutum na farko da Rahama Sadau ta fara tambaya da na tura mata account number na za ta yi min alheri, bayan mutane sun ga abunda ta fada akaina shine suka yi caa akanta da suma ta tura musu.
Sai ta kudiri aniyar yin giveaway ga wasu mabiyanta mutum 100 kuma ta cika alkawarinta.
Saidai kuma ta manta da ni da ta fara tambaya ta da na tura mata account nawa. Kuma ba ta tura min ba har yanzu. Ina fatan Allah Ya sa jinkirin ya zamar min alkairi. Idan babu rabo na kuma Allah Ya kawo min wani mafi alkairi.”
Bayan wallafa sakon abun ya baiwa mutane mamaki ciki harda ita jarumar hausaloaded ta tattauro martanin mutane kamar haka.
@Rahama Sadau tana cewa:
Idris Ka kwantar da hankali ka.
@Muhammad Ismail Ali cewa yake:
Allah wadaran da matsiyaci
@MB sulaiman shima ga abin da yake cewa:
Man Sagir.
Kamar Basune Kan Gaba Wajen Haramta Kudin Yan Films Ba, Kaga Yanzu Rige Rigen Neman 10k Na Wata Jaruma Sukeyi.
@kanuri Today cewa suke:
Aikin banxa, kufito kunemi halal naku yafi kudunga nema awajen bayi
Allah karabamu da mutuwar zuciya
Ba ita ba ko dangote ne yace zaiyi giveway saide nace Allah yabawa mai rabo Sa’a wajen Allah muke nema Alkah kabamu dan girmanka.