Yadda zaku cike Tallafin Noma: Shirin Kungiyar Matan Najeriya don Cigaban Noma (NWAP) - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Yadda zaku cike Tallafin Noma: Shirin Kungiyar Matan Najeriya don Cigaban Noma (NWAP)

Sep 24, 2024


Yadda zaku cike Tallafin Noma: Shirin Kungiyar Matan Najeriya don Cigaban Noma (NWAP


Domin samun tabbaci cikewa na musammanZa a tambaye ku wasu bayanai kamar haka:



1. Cikakken Sunanka


2. Nambar Wayarka


3. NIN Number (Lambar Shaidar Zama Dan Kasa)


4. Jiharka


5. Karamar Hukumarka


6. Mazabarka


7. Kalar Sana’arka


Muhimman Abubuwan da Ya Kamata a Lura:


- Ka cika dukkan bayanan da za a tambaya da cikakken bayani da kulawa.


- Lambar wayar da zaka yi amfani da ita wajen danna code ɗin *347*781# ta kasance ita ce ka yi rijistar NIN dinka, kuma ita ce ka yi rijistar BVN da asusun ajiyarka.


- Wannan tsari zai taimaka wajen saurin tantance bayanai, kuma zai saukaka wa gwamnati gudanar da tsare-tsaren tallafi cikin sauƙi.


 Wasu Muhimman Nasihu:


- Cika fom ɗin sau ɗaya kacal ya wadatar, sannan ka yi addu’a Allah ya bada sa'a.


- Idan kana da wasu mutane da suke bukatar tallafi, zaka iya cika musu fom dinka matuƙar suna da NIN Number koda ba su da asusun banki.


- Dangane da sana’a, a lokacin cike fom, zaka iya zaɓar sana’o’in kamar haka:



   - Noma


   - Kiwo


   - Dinki


   - Kwalliya (Cosmetics)


   - Kasuwanci


   - Saye da sayarwa


   - Kiwo na kaji ko dabbobi


   - Saloon


   - Wanzanci


   - Da sauransu.


- Ba lallai sai ka zabi wasu sana’o’i da suka fi karfi ko girma ba; ka duba na kusa da kai wanda kake da ilmi ko kwazo a ciki.


- Idan ka cika maka da kanka da matarka, ko budurwarka, ko yan uwanka da abokan arziki, ka tabbata suna da NIN Number, koda kuwa ba su da asusun banki.


Abin Lura: 

Bayan an cika fom din, za a ba da ID Number; ka adana wannan lambar saboda za a iya buƙatar ta nan gaba.