Ali Nuhu ne ya yi min aure, ya kuma ba ni jari, inji Alolo


Ali Nuhu ne ya yi min aure, ya kuma ba ni jari, inji Alolo


DARAKTA a Kannywood, Sheikh Isah Alolo ya bayyana cewa Manajin-Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Dakta Ali Nuhu, shi ne wanda ya yi masa aure, ya kuma ba shi jari.


Alolo ya bayyana haka ne a ‘Instagram’, inda yace, “Kai min aure ka ba ni jari. Duk wani abin alheri idan ya biyo ta hannun ka ko wanda ka ke da iko sai ka saka ni.


“Tun daga lokacin da na yi aure, duk lokacin da mu ka yi waya ko mu ka haɗu, sai ya tambaye ni ina fatan babu wata matsala ko?”


Daraktan ya cigaba da cewa, “Ya damu da ni sosai kamar yadda ɗan’uwa ya ke damuwa da ɗan’uwan sa.


“Ya girme ni, ya fi ni ɗaukaka da sauran abubuwa da yawa na rayuwa, amma duk da haka ya na girmama ni, ya na girmama alaƙa ta da shi.


“Ya na da tausayi, kawaici, haƙuri, yafiya da kuma halacci. Duk wanda ya rayu da shi ya san haka baya manta alheri.


“Mutane da yawa, wanda su ke wajen Kannywood, su kan yi tambaya wai me ya sa duk kannywood kowa ya ke girmama Ali Nuhu?


“Amsar ita ce: Kyawawan halayen sa da ɗabi’un sa, su ne su ka siya masa daraja. Duk wanda ka gani da mutunci shi ya siyawa kan sa ba aro ya yi ba.”


Alolo ya yi masa addu’ar cewa Allah ya yi masa tsari da tsautsayi da asara, mugun ji, mugun gani, sharrin mutum da na aljani, Allah ya tsare.


Ya ƙara da cewa, “Ina roƙon Allah duk wata kafa da maƙiyi zai kalla ya ga aibun sa Allah ya toshe masa ita. Kuka idan ba na daɗi bane, Allah ya hana idanuwan sa yi.


“Allah ya ƙara girma da ɗaukaka boss.”