Allah Sarki - Tsohuwar jaruma a Kannywood, Zulai Illah, ta riga mu gidan gaskiya
Allah ya ɗauki ran tsohuwar jaruma a Kannywood, Malama Zulaihat Ɗalhat, wadda aka fi sani da ‘Zulai Illah’.
Zulaihat, wadda matar jarumin Kannywood Shu’aibu Idris Lilisco ce, ta rasu a jiya Laraba, 23 ga Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 2:00 na rana, a Asibitin Nassarawa da ke Kano, bayan jinya da ta yi fama da ita.
An yi jana’izar ta da ƙarfe 5:30 a gidan mijin ta da ke unguwar Tudun Yola, daga nan aka kai ta gidan ta na gaskiya a maƙabartar Ɗandolo.
Marigayiyar ta rasu ta bar ‘ya’ya biyar da mijin ta.
Kafin ta auri Lilisco, Zulaihat mazauniyar Kaduna ce, kuma ta yi shuhura bayan fitowar ta a fim ɗin ‘Illah’ na kamfanin Koli Trading Company, Kaduna.
Zulaihat da Lilisco sun yi aure a ranar 13 ga Disamba, 2003, wato shekarar su 21 da wata goma.
Mutuwar ta ta girgiza jama’a matuƙa, ‘yan fim da waɗanda ba ‘yan fim ba. Jama’a na ta yi mata addu’ar samun rahama.
Allah ya jiƙan Zulaihat Ɗalhat da rahama. Allah ya albarkaci dukkan abin da ta bari.