Damar Cike Tallafin Shirin Keke Napep Mai amfani da Gas Mai suna presidential initiative (CNG) - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Damar Cike Tallafin Shirin Keke Napep Mai amfani da Gas Mai suna presidential initiative (CNG)

Oct 9, 2024


Damar Cike Tallafin Shirin Keke Napep Mai amfani da Gas Mai suna presidential initiative (CNG)


Kamar yadda kuka sani cewa Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin rabon kekuna masu amfani da iskar gas guda 2,000 domin tallafawa matasan Najeriya su shiga harkar sufuri mai tsada. Wannan shiri na musamman, wanda aka fi sani da Presidential CNG Initiative (Pi-CNG), na nufin rage radadin tsadar sufuri tare da bunkasa tattalin arzikin kasa ta hanyar samar da ayyukan yi da kuma amfani da makamashi mai tsafta wanda ba ya gurbata muhalli.


Wanda wannan shirin ya kunshi rabon kekunan napep masu amfani da iskar gas ga matasa domin su samu damar gudanar da harkokin sufuri cikin sauki da kuma araha. Wannan mataki yana da nufin rage yawan kudin sufuri, bunkasa kasuwanci, da kuma samar da hanyoyin dogaro da kai ga matasa a fadin Najeriya. 


Yadda Zaku Cike Wannan Tallafin Daga Gwannatin tarayya


Wannan tsari zai bai wa matasa damar shiga harkokin kasuwanci da kuma samun hanyar dogaro da kai cikin gaggawa. Duk wani matashi mai sha’awar shiga wannan shiri zai iya yin rajista ta tashar yanar gizo ta 


Ga link nan da zakuyi amfani dashi wajen Cike Wannan Tallafin fatan nasara a cikin Shi.

www.youthcng.ng 


Ko wannan link dayake a kasa 


www.pci.gov.ng/tricycle