Gwamnatin Tarayya ta saki kudi kimanin Naira biliyan 24.8b Wanda za'a rabawa adadin mutane 991,261 - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Gwamnatin Tarayya ta saki kudi kimanin Naira biliyan 24.8b Wanda za'a rabawa adadin mutane 991,261

Oct 2, 2024


Gwamnatin Tarayya ta saki kudi kimanin Naira biliyan 24.8b Wanda za'a rabawa adadin mutane  991,261 


Shirye Shiryen da Zasu Amfana da Wadannan Kudade Sune Kamar Haka👇👇


•RRR,

•CCT

•PVHH,

•NCTO,

•HUP


Za'a rabauta da samun Wannan kudi sau uku Wanda tini Wasu sun fara ganin nasu tin a farkon Wannan sati, Kuma biyan yana cigaba da gudana a yanzu haka.


Shirin ba sabo bane, Anyishi tin a lokacin Gwamnatin Buhari, Kuma tin a lokacin aka fara bawa dubban jama'a wadannan kudade,


Saidai yanzu an sabunta biyan, Kuma Duk Wanda ya sami Wannan kudin a Gwamnatin Buhari kai tsaye yasa rai da cigaba da samun wannan kudi in sha ALLAHU.


Hakama Wadanda aka tantance bayanansu kuma bayanan suka kasance daidai to in sha ALLAHU zasu sami Wadannan kudade.


Bari Mutina Muku hanyoyin da akabi aka cike Wannan shirin tin a farko.


Wasu Kai tsaye an turo musu code kai tsaye a layinsu na waya sun cike.


Wasu Kuma bayan code din unguwanni da garuruwa ya bayyana sunyi amfani da code din unguwa ko karamar hukumar su sun  cike.


Wasu an cike musu ta hanyar link amma ta hannun enumerator Wanda ake karbar bayanansu na bank Domin cikewa.


Wasu kuma gida gida aka bisu inda aka basu yellow da Blue din kati  dadai sauran hanyoyi makamantan haka.


Dubban Jama'a masu tarin yawa tin aka bude musu Account ta Bank Access Da Zenith Bank da sauran Bankuna da aka zaba a sauran jihohi  a karkashin Wannan tsari, Kuma tini an saka musu wannan kudade acikin account dinsu saidai ba'a bawa wasu damar fitar da kudin ba.


Wasu Kuma an tura kudin amma ba'a basu damar ganin alert din kudin ba, Yanzu Haka ATM daban daban masu tarin yawa sunanan angama aikinsu.


Za'a kira masu shi abasu domin fitar da kudinsu kai tsaye da aka saka musu ta account din da gwamnati ta amince abude musu tin a farko Domin shirin.


Amma Wadanda suka cike RRR tin farko da Wadanda aka karbi bayanan bankinsu kai tsaye wajan cikewa tin a farko, To zasu cigaba da ganin kudadansu kai tsaye ta cikin account dinsu tare da cire abinsu anan take.