Jarumi Adam A. Zango ya zama Darakta-Janar na gidan talbijin na Qausain a Kaduna
HUKUMAR Daraktocin gidan talabijin na Qausain ta naɗa shahararren jarumi kuma mawaƙi a Kannywood, Adam A. Zango a matsayin Darakta-Janar na gidan talbijin ɗin da ke Kaduna.
Shugaban gidan talbijin ɗin, Alhaji Nasir Idris, ya ba da sanarwar naɗin Zango a wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, 7 ga Oktoba, 2024 a Abuja.
Haka kuma ya bayyana cewa naɗin ya fara aiki a nan take.
A cewar sanarwar, an amince da naɗin ne a lokacin wani taro na musamman da hukumar daraktocin ta yi.
Alhaji Nasir ya ce, “An naɗa tsohon gwamnan Jihar Kano na mulkin soja, Kanar Sani Bello (mai ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar Daraktocin kamfanin.”
Sai dai kuma naɗin Kanar Sani Bello na tsawon shekara ne kamar yadda dokar kamfanin ta tanada.
Shugaban ya kuma ce, “An naɗa tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, a matsayin mai sa ido a kan shugabancin kamfanin.”
Ya kuma bayyana naɗin tsoron ma’aikacin BBC Hausa, Alhaji Ahmad Abdullahi, a matsayin daraktan zartarwa.
Daga ƙarshe, ya buƙaci waɗanda aka naɗa ɗin da su yi amfani da ƙwarewar su don ciyar da manufofin kamfanin gaba.