Kannywood tayi Rashi A’isha ‘yar furodusa Bello Achida ta rasu


Kannywood tayi Rashi A’isha ‘yar furodusa Bello Achida ta rasu


ALLAH ya yi wa A’isha ɗiyar furodusa kuma Mai Binciken Kuɗi (Auditor) na Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Bello Achida, rasuwa.


Malama A’isha ta rasu a daren Lahadi, 27 ga Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 2:00 na dare a Asibitin Janaral da ke Ƙaramar Hukumar Mafara a Jihar Zamfara, bayan haihuwar ta ta farko, inda ta haifi ‘ya mace.


Jinjirar ta rasu jim kaɗan bayan haihuwar ta, daga bisani mahaifiyar ta bi ta.


A’isha ta rasu ta bar mijin ta, Malam Murtala Adamu, da iyayen ta.


An yi jana’izar ta da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Litinin a gidan mijin ta da ke cikin garin Mafara.


Allah ya jiƙan ta da rahama.