Mawaki Rarara ya gina makarantun firamare uku a yankin su
Daya Daga cikin manyan mawakan siyasa a Kannywood, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), ya ƙaddamar da makarantun firamare guda uku waɗanda ya gina kyauta a wasu ƙauyuka uku da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanja ta Jihar Katsina.
An yi bikin ƙaddamar da makarantun ne a jiya Litinin, 7 ga Oktoba, 2024 a garin Kahutu, inda nan ne mahaifar sa.
Bikin ya samu halartar manyan mutane daga ƙaramar hukumar da kuma jihar.
Kamar yadda mai taimaka wa Rarara ta ɓangaren soshiyal midiya, Malam Rabi’u Garba Gaya, ya bayyana, an gina makarantun ne, ɗaya a Kahutu, ɗaya a Gidan Dari da ɗaya a Barmi, duk a ƙaramar hukumar.
Da yake jawabi a wurin bikin, Rarara ya ce, “Ilimi shi ne ginshiƙin al’umma, saboda haka iyaye su daure su turo ‘ya’yan su makaranta. Idan yara suka yi ilimi za a samu al’umma tagari.”
Ya ƙara da cewa, “Domin taimaka wa matasan da su ka yi karatu, amma ba su da aikin yi, zan ɗauki malaman makaranta a yankin mutum ɗari uku na wucin-gadi na tsawon wata shida. Amma in-sha Allahu nan gaba zan yi ƙoƙarin nema masu aiki na dindindin a gwamnati.”
Ɗimbin mutanen yankin da sauran jama’a sun yaba wa Rarara matuƙa kan wannan aiki da ya yi, suna yi masa fatar alheri.