Sabon Tallafin dogaro da Kai Daga Gwannatin tarayya
Ina matasan Najeriya! Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar da sabon Shirin ta mai taken “Renewed Hope Employment Initiative”. Wannan shirin zai samar da aikin yi da koyar da sana’o’i ga matasa 93,731 a faɗin Najeriya. Bugu da ƙari, zai bada jari na fara sana’o’in ga waɗanda suka samu horon, sannan kuma za a baiwa wasu damar samun lamuni dan gudanar da ƙananu da matsakaitan kasuwanci.
Shirin na daga matakin da Gwamnatin ke ɗauka don wadata ƴan Najeriya da aikin yi, ƙarfafa dogaro da kai da kuma bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar.
Masu buƙata zasu iya shiga adreshin yanar gizo ta intanet kamar haka;
APPLY HERE
Abubuwan da ake buƙata domin yin rejista; Asusun Email, hoton fasfo, nambar shedar ɗan ƙasa NIN.
Za a tuntubi waɗanda aka zaba kai tsaye ta kan adreshin Email din da sukai rejista da shi. Sannan kuma akwai alawus da za a baiwa dukkan waɗanda za a baiwa horon a faɗin ƙasar nan.
An fara rejista a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, 2023, za kuma a rufe a ranar Talata 31 ga watan Disamba, 2024.
Kada ku bari ayi babu ku.