An raɗa wa ‘yar Fati Ladan suna Raliya Allah ya raya
A YAU Talata, 12 ga Nuwamba, 2024 aka yi bikin raɗa wa ‘yar tsohuwar jaruma a Kannywood, Fati Ladan, wadda ta haifa a makon da ya gabata suna.
An raɗa wa jaririyar suna Raliya, amma za a riƙa kiran ta da Ihsan.
An yi raɗin sunan ne da safe, a gidan su mai lamba, 4 Yarima Close, kan Titin Jinya, daura da Kanta Road, Kaduna.
Da misalin ƙarfe 3:00 na rana kuma aka shirya ƙasaitaccen walima ga ‘yan’uwa da abokan arziki don taya Fati da mijin ta Yerima murna.
Da ya ke dukkan su na da jama’a, gidan na su ya cika maƙil da ‘yan’uwa da abokan arziki.
An ci, an sha, kuma an gyatse. Domin kuwa, abinci da abin sha sai da aka bar su.
Bayan kowa ya gama goge wuyar sa, sai mai jego da mijin ta su ka fito, inda aka ɗauki hotuna
Mutane da dama sun halarci walimar. Daga cikin su akwai manyan abokan Yerima Shettima daga wurare daban-daban, ‘yan ƙungiyar ‘Arewa Youth Consultative Forum’ reshen Jihar Kaduna, iyalan furodusa a Kannywood, Yakubu Lere, wato Hajiya Safiya, Hajiya Habiba da Hajiya Saudat. Sai kuma Hajiya Wasila Isma’il.
Allah ya raya Raliya, ya kuma albarkaci rayuwar ta.