Buri na in auri marubuci ɗan’uwa na, inji marubuciya Gimbiya Rahama - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Buri na in auri marubuci ɗan’uwa na, inji marubuciya Gimbiya Rahama

Nov 23, 2024


Buri na in auri marubuci ɗan’uwa na, inji marubuciya Gimbiya Rahama


Marubuciya Rahama Ahmad Muhammad, wadda aka fi sani da Rahama Gimbiya a fagen rubutu, haziƙar matashiya ce wadda tauraron ta ke haske a yau. Ta kasance marubuciya mai kaifin basira, wanda hakan ya sa ta samu karramawa daga ƙungiyoyi da dama.


Mujallar Fim ta samu damar zantawa da Gimbiya Rahama, inda ta feɗe mana biri har wutsiya game da tarihin ta, yadda ta tsinci kan ta a harkar rubutu, burin ta, yaren ta, da sauran su.


FIM: Ki faɗa mana tarihin rayuwar ki a taƙaice.


Gimbiya Rahama: Da farko suna na Rahama Ahmad Muhammad, wadda aka fi sani da Gimbiya Rahma a fagen rubutu. An haife ni a garin Kano, cikin tsakiyar birni. Na yi makaranta tun daga firamare har zuwa sakandire haɗe da makarantar allo da Islamiyya tare da makarantar gaba da sakandire duk a cikin garin Kano.


FIM: Menene burin ki game da rubutu?


GIMBIYA RAHAMA: Babban buri na a harkar rubutu na auri marubuci, kuma na ci gaba da cin gajiyar sa har ƙarshen rayuwa ta.