Mawaƙi a Kannywood, Auta Waziri zai angwance


Mawaƙi a Kannywood, Auta Waziri zai angwance


Shahararren mawaqin nan na Kannywood, Mai suna Abdullahi Abubakar, wanda aka fi sani da Auta Waziri, zai yi bankwana da kwanan sitidiyo.


Za a ɗaura auren Auta Waziri da abar ƙaunar sa Halima Mustapha (Marmah), ranar Juma’a, 6 ga Disamba, 2024 da misalin ƙarfe 1:00 na rana a masallacin Juma’a na SMC, Unguwar Dosa, Kaduna.


Za a gudanar da ƙasaitaccen walima a ɗakin taro na Umaru Musa ‘Yar’adua da ke dandalin Murtala Square, Kaduna.


Allah ya kaimu da rai da lafiya, ya kuma bada ikon zuwa, gayyata zuwa GA kowa da yakeda lokaci.