Mawaqin Rarara zai gina masallaci a Sumaila
Mawaƙi Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) zai gina masallaci a garin Sumaila da ke Jihar Kano.
Mai taimaka wa mawaƙin a ɓangaren soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, shi ne wanda ya ba da sanarwar haka a soshiyal midiya.
Gaya ya ce, “Al’ummar garin Kuderi da ke Ƙaramar Hukumar Sumaila sun roƙi mai girma shugaban ƙasar mawaƙan Nijeriya, Alhaji Dauda Kahutu Rarara, da ya rushe babban masallacin garin ya gina musu wani sakamakon lalacewar da masallacin ya yi.”
M“Ya karɓi koken su, kuma in-sha Allahu zai rushe masallacin ya gina musu sabo irin na zamani nan da ƙaramin lokaci.”
Haka kuma sun ƙara roƙon sa da ya taimaka ya gyara masu magudanan ruwan garin domin da damina ruwa har gidaje yake shiga musu.
Nan take mawaƙin ya amince zai yi gyara musu.
Al’ummar garin Kuderi sun yi wa Rarara godiya tare da addu’ar Allah ya raba shi da Hajiya lafiya.