Yadda Zakayi Register Na CAC Da Kanka
A yau zamuyi bayani akan yadda zakuyi Register na CAC da kanku wato yadda zaku mallaki CAC Certificate.
Mene yasa akeyim Registration na CAC.
Shi CAC yanada matukar amfani fiyeda yadda mutum yake tunani saboda idan bakayi wannan registration dinba kuma zaka rasa abubuwa da yawa wani lokacimma zai iya kaika gidan yari idan case ya hadaaka da hukuma.
Ba kamar yadda mutane suka daukaba cewa amfanin CAC kawai shine don cika tallafi koneman bashin gwamnatin tarayya a a ba iya wannan bane amfaninsa amfaninsa yanada matikar yawa da saikayi zaka sani kadan daga ciki:
- Zaka iya samun bashin gwamnatin tarayya koh na jaha mai waya
- Zaka iya samun bashin daga banki
- Zaka iya samun tallafi kyauta daga gwamnati koh kungiyoyi
- Zaka iya kare kanka dashi idan hukuma ta tambayeka shedar registan kasuwancinka
- Zai bawa customers naka daman yadda dakai idan kuma wani ne kakeson kufara kasuwanci zai iya shiga ya dubah yaga saboda KYC know your customer
Da farko idan kanason yin registan CAC akwai wasu hanyoyi kamar haka:
- Na farko zakaje office dinsu inkaso
- Na biyu kaje cafe inkaso
- Na uku shine wanda zakayi da kanka inzaka iya
Yadda zakayi Registration na cac da kanka a wayanka
Da farko zaka shiga https://www.cac.gov.ng/ home page zai budema saika shiga inda akasa online registration kamar yadda zaka gani a kasa
Kana shiga zai budema acan kasa zakaga inda aka rubuta register ta gefe saika taba zai budema wurin login amma kai tunda sabone bazaka taba nan bah saika dubah inda aka rubuta SIGN UP saika shiga