Yadda zaku cike Tallafin Hukumar Kula Da Ayyukan Yi (NDE) Matasa 93,731 ne zasu samu Tallafin - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Yadda zaku cike Tallafin Hukumar Kula Da Ayyukan Yi (NDE) Matasa 93,731 ne zasu samu Tallafin

Nov 10, 2024


Yadda zaku cike Tallafin Hukumar Kula Da Ayyukan Yi (NDE) Matasa 93,731 ne zasu samu Tallafin


Tsarin Shirin da Kuma Ayyuka na na tallafin da matasa 93,731 zasu Samu su amfana da Shi.


A bisa tsarin Renewed Hope Agenda na Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu wanda ya maida hankali kan bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da rage talauci, Hukumar NDE ta kaddamar da shirin koyar da sana’o'i daga watan Oktoba zuwa Disamba 2024 domin samar da ayyuka 93,731. Wannan shiri ya ware nau'ukan sana’o'i guda 30 domin amfanin wadanda za su ci gajiyar shirin. 


Shirin yana da manufar yakar rashin aikin yi a Najeriya tare da samar da yanayin da zai inganta samun kudaden shiga. Domin isar da tallafin zuwa ga talakawa da kuma tabbatar da kowa ya amfana, NDE tana aiwatar da shirin a matakin mazabu na siyasa.


Lokutan farawa da kammala wannan Shirin:


  • Fara shiri: 14-10-2024

  • Kammala shiri: 31-12-2024


Yadda zaku cike tallafin Kia tsaye!!


Domin cikewa zaku latsa shafin yanar gizo gizo dake a kasa 


https://nderegistrationportal.ng/client-programs/information/1


Yadda zakuyi Rijista da wannan tallafin:


1. Cikakkun Bayanai na Kai (Personal Details):


  •    Hoto (ya kasance Daya Daga cikinsu jpeg/png/jpg, Kar ya wuce 1MB)

  •    Lambar NIN

  •    Sunan Gida

  •    Sunan Tsakiya

  •    Sunan Farko

  •    Jiha ta zama

  •    Karamar Hukuma (LGA)

  •    Mazabar Siyasa

  •    Lambar waya

  •    WhatsApp

  •    Ranar Haihuwa

  •    Jinsi

  •    Matsayin Aure


Allah yabada Sa'a da rabo !!